Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sakataren kwamitin ganin wata na fadar sarkin Musulmi Farfesa Wali Junaidu ya sanyawa hannu kuma aka rabawa manema labarai a Sokoto .
Sanarwar ta ce al’ummar musulmin Najeriya za su cika Azumi guda 30 a bana, don haka ya bukaci al’ummar musulmi su dauki Azumin gobe Talata.
Sanarwar tace Laraba 10 ga watan Afrilu 2024 ita ce za ta Kasance 1 ga watan Shawwal 1445.
Sarkin Musulmi ya kuma yi addu’ar Allah ya karɓi ibadu da addu’o’in da al’ummar musulmi Najeriya suka yi a cikin wannan wata na Ramadan.
