Featured
Gwamnan Kano Ya Taya Al’ummar Musulmi Murnar Barka Da Sallah
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya bukaci mazauna jihar da su rungumi halayen tausayi, karamci, da’a, kishin kasa, da zaman lafiya domin ci gaban jihar da kasa baki daya.
Gwamnan ya bayyana haka ne a sakonsa na Sallah a Kano ranar Laraba, inda yace ya kamata kowa ya ci gaba da koyi da irin wadannan kyawawan halaye har gaban watan Ramadan.
A yayin da yake taya daukacin al’ummar jihar da Shugaba Bola Tinubu da daukacin al’ummar Musulmi murnar kammala azumin watan Ramadan, Gwamnan ya sake nanata aniyarsa ta cika alkawuran da ya dauka yayin yakin neman zabensa.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana kwarin gwiwar cewa, ‘bayan wuya sai daɗi’, inda yace, gwamnatinsa ta shirya aiwatar da manyan ayyukan raya kasa a shekarar 2024.
