Featured
EFCC Ta Kama Tsohon Ministan Jiragen Sama Hadi Sirika

Rahotanni sun nuna cewa Hukumar EFCC mai yaki da masu karya tattalin arziki ta kama tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika.
EFCC ta kama Sanata Hadi Sirika ne kan zargin badakalar Naira biliyan 8.06 a zamanin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Wasu jami’an hukumar sun ce an kama shi ne a ci gaba da binciken da EFCC ke yi kan ma’aikatar sufurin jiragen sama a lokacin shugabancinsa.
Hadi Sirika yana fuskantar zargin almundahanar kwangila, karkatar da kudade, amfani da ofishinsu ta hanyar da ba ta dace ba da kuma safarar kudaden haram.
Bayanai sun bayyana cewa a ranar Talata ne EFCC ta tsare shi, bayan ya gabatar da kansa a babban ofishinta da ke Abuja domin amsa tambayoyi.