Connect with us

Featured

‘Yan Bindiga Sun Hallaka Mutane Uku, A Kokarinsu Na Sace Sarkin Zurmi

Wasu ’yan bindiga sun kai hari fadar Sarkin Zurmi, Alhaji Bello Muhammad Bunu, inda suka kashe mutane uku suka yi awon gaba da wasu.

Jaridar Aminiya ta tabbatar da cewa mutane ukun da aka kashe sun hada da Sarkin Gidan Masarautar Zurmi, Alhaji Yusuf Buhari da wani mai shayi da ke kusa da fada, da wani mutum guda.

Mazauna yankin sun ce bayan fadar sarkin, maharan a daren Laraba, sun kai hari gidan tsohon shugaban mulkin soja na Jihar Nasarawa, kuma tsohon ministan muhalli a gwamnatin Olusegun Obasanjo, Kanar Bala Muhammad Mande mai ritaya.

Shaidu sun ce a lokacin da aka kai harin Kanar Mande mai ritaya ba ya gida, amma Sarkin Zurmi na cikin fadarsa lokacin da ’yan bindigar suka kaddamar da harin.

A yayin harin, ’yan bindigar sun lalata turken sadarwa, sannan suka kone wasu injina guda biyu da ke kusa da fadar sarkin.

Wani mazaunin garin da ya nemi a boya sunansa, ya shaida wa wakilinmu cewa, daga shigowar maharan garin suka nufi gidan sarkin suka buɗe wuta a babbar kofar gidan a kokarinsu na samun shiga fadar domin sace sarkin.

Ya ce: “Inda Allah Ya kiyaye shi ne, an kulle kofar, amma ba don haka ba, da sun samu shiga cikin fadar, domin shi suka zo nema”.

Ya ce a kwanakin baya ma ’yan bindigar sun kai wa sarkin farmaki, amma sai Allah Ya kiyaye shi.

“A zahirin gaskiya ma, sarki ya dawo gari ne a ranar Litinin bayan yunkurin sace shi na farko bai yi nasara ba.

“A sirrance aka sa sarkin ya koma Gusau, inda ya shafe mako guda a can,” in ji shi.

Wani mazaunin garin kuma ya ce da maharan sun kasa samun shiga fadar, sai suka koma gidan tsohon sojan, suka yi ta harbe-harbe a kofar gidan, suka lalata abubbuwa da yawa.

Muhammad Inuwa, wani ɗan Zurmi ya ce yana shirin mayar da iyalansa Gusau saboda ba zai iya jure halin baƙin ciki da tashin hankalin da mazauna yankin ke ciki ba sakamakon hare-haren da ’yan bindiga ke kaiwa.

Ya ce: “Na gaji…Muna cikin bala’i da tawayar tattalin arziki ga kuma tashin hankalin ’yan fashi. Nauyin ya yi min yawa. Ba zan iya jurewa ba.

Kwamishinan ’yan sandan jihar Zamfara, Muhammad Shehu Dalijan, ya tabbatar da faruwar harin amma ya ce ba shi da masaniyar cewa an kashe wasu mutane.

Sai dai ya tabbatar da cewa ’yan bindigar sun sace daya daga cikin dogaron Sarkin Zurmi.

“Ba a fadar sarki a ka sace shi ba, a cikin gari ne aka ɗauke shi,” in ji kwamshinan ’yan sandan.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet