Featured
Masu Adaidaita Sahu Sun Kara Farashin Kudin Sufuri, Yayin Da Fetur Ya Kara Tsada

Masu baburan A Daidaita Sahu a Kano sun yi karin farashin kudin fasinja saboda tsadar man fetur da aka samu a Kasar nan, inda masu bumburutu ke sayar da galan daya a kan Naira 5,000.
Fasinjoji sun danganta karin kudin da aka samu da kimanin rabi kan wahalar man fetur da ake fama da ita a sassan kasar.
Wani fasinja ya bayyana cewa Naira 300 ya biya daga tsohuwar Jami’ar Bayero (BUK) zuwa titin Gidan Zoo, maimakon Naira 200 da ya saba biya kafin yanzu.
Yadda Zaman Kotu Kan Zargin Rashawar Ganduje Da Iyalansa Ya Kasance
Wata mace fasinja ta ce Naria 200 aka caje ta kudin A Daidaita Sahun zuwa wurin da ta saba biyan N100.
Tashin farashin litar fetur zuwa sama da Naira 1,000 shi ne babban dalilin wannan tsadar kudin sufuri, a cewar fasinjojin.
Kakaki24 TV ta rawaito cewa, Daga unguwar Ja’en zuwa Hotoro ya koma Naira 500 Mai makon Naira 300 da a baya ake biya.
Yan bumburutu sun koma sayar da galan guda na man fetur a kan Naira 5,000, yayin da masu bumburutu dauke da jarkoki suke kokawa da masu ababen hawa domin samun shiga gidajen mai.
Wata mijiya ta ce Wadansu daga cikin ‘yan Burnnburutu sukan bayar da nagoro domin su samu man da suke zuwa su sayar da matukar tsada.