Addini
Aikin Hajji: Za A Fara Jigilar Maniyyatan Nijeriya Zuwa Kasa Mai Tsarki

Hukumar Kula da Aikin Hajji ta Kasa (NAHCON) ta sanar da cewa ranar 15 ga watan nan da muke ciki na Mayu za a fara jigilar maniyyata zuwa kasar Saudiyya.
Shugaban Hukumar NAHCON, Jalal Ahmad Arabi, ne ya sanar da haka a taron masu ruwa da tsaki kan aikin Hajji da Umrah da ya gudana a Abuja a ranar Alhamis din nan.
Jalal Arabi ya ce a bana maniyyata kimanin 65,500 ne za su sauke farali daga Najeriya, inda za su shafe akalla kwanaki hudu domin yin ziyara a Madina kafin fara aikin Hajji.
Shugaban hukumar ya bayyana cewa za a yi jigilar maniyyata ne daga cibiyoyi 10 na fadin Kasar nan.