Featured
Kano: Hukumar Hisbah Ta Ware Gurbi 50 Ga ‘Yan Jarida A Shirin Auren Gata

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ware wa Ma’aikatan Jarida gurbin mutane 50 a sabon shirin Auren gata da za a sake yi a jihar.
Babban Kwamandan Hukumar Hisbah ta Jihar Kano Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ne ya bayyana hakan a wata hira da manema Labarai.
Sheikh Aminu Daurawa ya ce Hukumar ta ware wa ‘yan Jarida gurbin ne domin kyautata alaka da ma’aikatan yada Labarai a jihar.
Duk da dai vai bayyana lokacin da za a sake gudanar da auren ba, amma ya ce za a ware wa bangarori kamar masu Damara, ‘Yan jarida da sauransu gurabe domin karfafe dangantaka.