Connect with us

Featured

Dakarun Sojin Jamhuriyar Nijar Sun Kama Jagoran ‘Yan Bindigar Najeriya

 

Dakarun sojin Jamhuriyar Nijar sun kama wani jagoran ’yan bindigar Najeriya, Kachallah Mai Daji a kusa da iyakar garin Illela da ke kasar.

Wani Masani a fannin harkar tsaro kuma mai sharihi kan yaki da tayar da kayar baya a yankin tafkin Chadi, Zagazola Makama, ya ce sojojin Nijar sun kama dan bindigar ne a lokacin da yake kokarin sace dabbobi ya tsallaka iyakar Najeriya da Nijar da su.

“Sojojin Nijar sun damke shi yana kokarin satar dabbobi a kan iyakar Najeriya da Nijar,” in ji shi.

Zagazola ya bayyana Kachallah Mai Daji a matsayin daya daga cikin hatsabiban yan bindiga da suka shafe shekaru suna addabar yankin Arewacin Kasar nan.

A cewarsa, “dan ta’addan ya shafe kusan shekara 10 yana kashe mutane da kona kauyuka da sace jama’a da ma kakaba musu haraji a kauyukansu.”

Kachalla Mai Daji dai ya fi addabar kauykan yankin Illela da suka hada da Tozai, Sabon Garin Darna, Darna Tsolawo, Tudun Gudali, Basanta, Ɗan Kadu, Takalmawa, Gidan Hamma, Ambarura, Gidan Bulutu da sauran makwabtansu.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet