Featured
Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Jami’ar CUSTEC A Jihar Kogi Tare Da Sace Dalibai Da Dama

Ana zargin wasu Ƴan bindiga sun sake kai hari jami’ar kimiyya da fasaha ta CUSTEC da ke jihar Kogi tare da sace wani adadi mai yawa na ɗalibai, sai dai har yanzu mahukunta basu tabbatar da faruwar wannan farmaki ba.
A cewar wasu shaidun gani da ido ƴan bindigar sun yi dirar mikiya a jami’ar ta CUSTEC da ke yankin Osara a garin Okene ne da misalin karfe 9 na daren jiya Alhamis, kuma har yanzu ba a gama tantance yawan daliban da suka sace ba.
Bayanai sunce harin ƴan bindigar ya faru ne a dai dai lokacin da dalibai suka taru a dakunan daukar jarabawa don yin nazarin karatuttukansu dai dai lokacin da jarabawa ke karatowa.
Wani ganau ya ce ƴan bindgar kwatsam suka shigo daga dazukan da ke zagaye da makarantar tare da fara harbin isaka bayan sun yi wa jami’ar ƙawanya.
A cewar majiyoyi da farko ƴan bindgar sun tattara daliban a dakunan jarabawa gabanin fara tisa keyarsu don shiga daji dasu, gabanin isowar jami’an tsaron sa kai wadanda suka yi hadin gwiwa da jami’an tsaron makarantar don tunkarar ƴan bindigar.
RFI ta rawaito cewa Majiyoyin sun ce jami’an tsaro sun yi nasarar daƙile yawan ɗaliban da ƴan bindigar suka ɗiba.
A ranar 13 ga watan nan ne jami’ar ta kimiyya da fasaha a jihar Kogi ke shirin fara jarabawa.