Connect with us

Featured

Filato: Ƴanbindiga Sun Hallaka Makiyaya 2 Da Shanu 150

Rahotanni sun ce aƙalla makiyaya biyu da shanu 150 wasu ‘yan bindiga sun kashe a wani hari da suka kai gundumar Kwal da ke Ƙaramar hukumar Bassa a Jihar Filato.

A cewar shugabannin Fulani a jihar, an kuma yi awon gaba da shanu sama da 100 a lokacin faruwae lamarin.

Shugabannin Ƙungiyar Miyetti Allah (MACBAN) da na takwararta Gan Allah Fulani (GAFDAN), Nura Abdullahi da Garba Abdullahi, sun tabbatar wa majiyarmu faruwar lamarin a ranar Juma’a.

Sun bayyana cewa akwai yiwuwar adadin shanun da aka kashe su haura 150, yayin da wasu da dama suka ɓace.

Da yake bayyana lamarin, shugaban GAFDAN ya ce, “Makiyayan suna kiwon shanunsu ne da misalin ƙarfe 9:00 na safiyar Laraba, kwatsam wasu ‘yan bindiga suka buɗe musu wuta.

“Sun harbe makiyaya biyu har lahira. Haka Kuma yau, sun harbe ɗaruruwan shanu, inda suka kashe kimanin 150.

“Har yanzu ba mu tabbatar da yawan ɓarnar ba, domin lamarin ya faru ne a wani wuri mai nisa da ke da wahalar shiga, ba tare da jami’an tsaro ba. Mun yi babban rashi.

“Lokaci ya yi da jami’an tsaro za su ɗauki mataki kan ta’asar da ake yi wa mutanenmu.

“A duk lokacin da aka kai mana hari, sai jami’an tsaro su nemi mu kwantar da hankalinmu.

“Wannan yunƙuri ne na halaka mu, kasancewar hari ne na ba gaira ba dalili. Muna kira ga hukumomin tsaro da su kawo mana agaji.”

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet