Connect with us

Featured

Gwamnan Kano Ya Biya Kudin Rijistar Daliban Jami’a Guda 1,740

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya biya kudin rijistar sabbin dalibai 1,740 da suka samu gurbin karatu a jami’ar ilimi ta Saadatu Rimi da ke Kumbotso mallakin gwamnatin jihar.

Gwamnan ya bayyana haka ne a ranar Asabar a lokacin kammala karatun digiri na farko na makarantar.

A shekarar 2023 ne Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ta amince da sabunta Kwalejin Ilimi ta Sa’adatu Rimi da ke Kumbotso a Jihar Kano zuwa jami’ar ilimi.

Ya ce gwamnatin jihar ta himmatu sosai wajen tallafawa bukatun ilimin dalibai ba tare da la’akari da siyasa ba.

Ya ce gwamnatin jihar ta kuma ware kashi 30 cikin 100 na kasafin kudinta na shekarar 2024 ga ilimi, wanda hakan ya nuna samu karin kan shekarun baya.

Kwamishinan ilimi mai zurfi na jihar Dr Ibrahim Kofarmata ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta yafe kashi 50 na kudaden makaranta na makarantun sakandire da manyan makarantun jihar domin samun saukin ilimi ga yara masu rauni.

Shugaban Shugaban Jami’ar Farfesa Yahaya Isa Bunkure, ya yabawa kwazon Gwamna Abba wajen bayar da ilimi tare da bayyana irin nasarorin da jami’ar ta samu, da suka hada da shirye-shiryen bunkasa ma’aikata, ayyukan bincike, da inganta ababen more rayuwa.

Yahaya Bunkure ya ja kunnen daliban da suka kammala karatunsu da su himmatu da azama, tare da sanin muhimmancin zamansu a jami’ar.

Bunkure, ya kuma samu lambar yabo ta Fellowship daga Cibiyar Nigerian Institute of Physics (FNIP) saboda gudunmawar da ya bayar a fannin da jajircewarsa wajen bincike da ilimi.
(NAN)

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet