Featured
Adadin Wadanda Suka Rasu Ya Karu Cikin Mutanen Da Aka Kona A Masallachi

Rahotanni na bayyana cewa yanzu haka an samu karin mutane biyu daga cikin mutane sama da 20, bayan mutum na farko da ya rasu da wani matashi ya cinnawa Wuta.
Matashin ya cinnawa Mutane wuta ne a cikin wani masallaci a unguwar Larabar Abasawa da ke ƙaramar hukumar Gezawa a Kano sun rasu.
Wani mazaunin garin ya shaidawa Dala FM Kano, a ranar Larabar nan cewar, daga cikin mutane ukun da suka rasu har da limamin da ya jagorancin sallar asubar wannan rana, wanda a lokacin ne matashin ya cinna musu wutar lamarin da jikin su mutanen sama da 20 ya sassaɓule.
Idan dai ba’a manta ba matashin ya cinnawa mutanen wuta ne bayan da ya watsa Fetur cikin masallacin yayin da suke tsaka da sallar Asubah, ta wannan rana, wanda tuni jami’an tsaron ƴan sanda suka cika hannun su da shi.
Matashin dai ya ce ya cinnawa mutanen wutar ne biyo bayan wata magana da suke faɗa masa wanda ransa baya daɗi, ina ya sayo Fetur a cikin wani Galan lamarin da yaje ya kunna musu wutar, duk da shima hannayen sa biyu sun ƙone.