Connect with us

Featured

Ministar Mata Ta Dakatar Da Dan Majalisa Daga Aurar Da ‘Yan Mata 100 A Neja

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Neja, Barista Abdulmalik Sarkindaji, ya janye aniyarsa ta aurar da marayu 100 a mazabarsa.

Shugaban majalisar ya fasa aurar da marayun ne bayan ministar harkokin mata, Uju Kennedy-Ohanenye, ta nuna damuwa game da ko an tabbatar da amincewar ’yan matan da shekarunsu, kamar yadda doka ta ayyana.

Sarkindaji ya bayyana wa manema labarai hakan ne a harabar majalisar a ranar Talata, inda a cewarsa ya gama shirye-shiryen daurin auren, har ya biya kudin sadaki a madadin angwaye.

Abdulmalik Sarkindaji ya ce ya bar wa shugabannin gargajiya da na addinin yankin amanar daurin auren, ya ba su dama su yanke hukunci kan batun, amma shi ya hakura tun da abin ya janyo ce-ce-ku-ce.

Honaabul Barista Abdulmalik Sarkindaji ya bayyana rashin jin dadinsa da matakin na ministan mata ta Najeriya, ya ce bai tilastawa ‘yan mata auren ba.

Ya ce iyayen yaran ne suka tuntube shi don neman tallafi, ya kuma yanke shawarar daukar nauyin auren ne bayan ya tuntubi malaman addini da shugabannin gargajiya, da sauran masu abin cewa kan harkokin jama’a kafin ya amince.

Shugaban majalisar ya sa an zabo mata 100 daga cikin 270 da ke son aure amma babu hali.

Ya kuma caccaki ministar kan yadda ta rika yada batun a kafafen sada zumunta ba tare da ta tuntube shi domin sanin gaskiyar lamarin ba.

Ya bukaci ta ziyarci sansanonin ’yan gudun hijira a jihar Neja domin fahimtar kalubalen da ’yan matan da iyayensu ke ciki.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet