Connect with us

Featured

Sarkin Gaya Ya Bada Naira Miliyan 3 Ga Wadanda Gobara Ta Kona A Masallaci 

Sarkin Gaya Alhaji Aliyu Abdulkadir ya bada gudummawar naira miliyan uku ga wadanda ibtila’in gobara ya shafa a masallaci a garin Larabar Abasawa dake karamar hukumar Gezawa a jihar Kano.

Sarkin ya bada gudummawar a ranar juma’ah yayin ziyarar da ya kai Asibitin Murtala inda wadanda ibtila’in ya shafa suke karba magani, sannan ya bukaci sauran Alummah da su taimaka musu ta kowacce hanya.

“Muna mika sakon jajen mu ga iyalai da yan uwan wadanda wannan ibtila’i ya shafa, sannan masarautar Gaya zata bada duk wani goyon baya ga wadanda wannan hatsari ya shafa wajen ganin sun samu lafiya ingantacciya”.

Dagacin Gezawa mai unguwar mundubawa Alhaji Mahmud Yusuf ya yabawa Sarkin wajen karamcin sa da nuna goyon bayan sa ga Al’ummah.

A nasa bangaren shugaban kwamitin riko na karamar hukumar Gezawa, Muhammad Tanko, ya tabbatar da mutuwar mutane 13 yayin da mutane 12 suke cigaba da karbar kulawa a hannun likitoci.

A karshe ya bukaci Al’ummar yankin su zama masu sa ido da lura da duk wani motsi a yankin, sannan yayi alqawarin gyara masallacin da aka lalata nan kusa ba tare da bata lokaci ba.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet