Featured
Za Mu Bi Umarnin Babbar Kotun Tarayya Kan Masarautu -Kwamishinan Yansanda

Rundunar Yansandan jihar Kano ta sha alwashin yin aiki da umurnin wata babbar kotun tarayya da ta haramta wa gwamnatin jihar Kano aiwatar da dokar da aka soke da ta shafi masarautar Kano.
Wannan umarnin kotun, wanda mai shari’a Mohammed Liman ya bayar, ya haramtawa Gwamna Abba Yusuf mayar da Sarki Muhammadu Sanusi II kan mukaminsa, tare da dakatar da soke masarautun Bichi da Gaya da Ƙaraye da kuma Rano.
CP Usaini Gumel ya ce jami’an tsaron suna biyayya ne da umarnin da kotun tarayyar da ke Kano ta bayar.
Don haka CP Gumel ya ce jami’an ‘yan sanda tare da haɗin gwiwar sojoji da sauran jami’an tsaro za su yi aiki tare domin samar da cikakken tsaro kamar yadda kundin tsarin Najeriya ya tanadar.