Featured
Mun Soke Hawan Sallah Ne Don Wanzuwar Zaman Lafiya – Aminu Bayero

Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya aike da saƙon fatan alheri ga Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu da Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, sakamakon zuwan bikin sallah babba.
Sarkin, ya kuma bayyana cewa, an soke bikin hawan sallah na bana ne bisa shawarwarin da aka bayar gane da tsaro, domin wanzar da zaman lafiya a jihar.
Aminu Ado, a yi waɗannan kalamai ne a yau Asabar ta cikin wani shiri na kai-tsaye da aka yaɗa daga ƙaramar fadar Nassarawa.