Featured
Kaduna: Shugabannin Mabiya Addinin Kiristanci Sun Ziyarci Musulmai A Yayin Sallar Idi

A wani yunkuri na tabbatar da hadin kai tsakanin mabiya addinai, wani shugaban mabiya addinin Kirista a jihar Kaduna, Pasto Yohana Buru, ya gabatar da jawabi kan muhimmancin zaman lafiya ga dubban al’ummar Musulmi da suka halarci Sallar Idi.
An gudanar da Sallar ne a filin Murtala Mohammed Square wanda aka bayyana muhimmancin hadin kai da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai a Najeriya.
Pasto Buru, wanda shi ne shugaban cocin Christ Evangelical and Life Intervention ya jagoranci tawagar Kiristoci wajen kai ziyara ga Musulmai.
Wannan dai shi ne karo na 3 a ziyarar da yake kaiwa.
Yayi bayanin cewa irin wannan ziyara na bada damar tattaunawa da fahimtar juna.
“Mun taya mai Alfarma Sarkin Musulmai, Alhaji Sa’ad Abubakar murna da Sheikh Dahiru Bauchi da Sheikh Ibrahim Yakubu El-Zazzaky da Sheikh Ahmad Mahmud Gumi da sauran malamai”, inji Pasto Buru.
Ya ce a yayin bikin Kirismeti Musulmai daga kungiyoyi daban daban sun taya su murna.