Featured
Abba Gida Gida Ya Bai wa Alhazan Kano Riyal 100 A Matsayin Goron Sallah

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya baiwa Alhazan Kano 3,121 a matsayin Goron Sallah.
Mai magana da yawun mataimakin Gwamnan Kano, Ibrahim Garba Shu’aib ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin.
Ibrahim Garba ya ce mataimakin Gwamnan Kano, Aminu Abdussalam Gwarzo ne ya sanar da bada Goron Sallar a yayin ziyarar da ya kai sansanin Alhazan dake Mina a kasar Saudia.
A cewarsa, ba wannan ne karo na farko ba da Gwamnan ya bai wa Alhazan kyauta inda tun da fari ya cika wa kowanne Alhaji Naira dubu 500 kudin tafiya aikin Hajjin da kuma Naira dubu 150 a matsayin kudaden da za su yi guzuri da shi.
A gefe guda kuma shugaban katafaren shagon Sahad Store, Alhaji Mijinyawa ya bai wa Alhazan na Kano kyautar Riyal 50 kowannensu.
Mataimakin Gwamnan na Kano yayi kira ga Alhazan da su yiwa Kano da Najeriya addu’a.