Featured
Mahaifiyar Abubakar Bukola Saraki Ta Rasu

Allah ya yiwa Mahaifiyar tsohon shugaban majalisar dattawa, Dr. Abubakar Bukola Saraki, Florence Morenike Saraki, rasuwa tana da shekaru 89.
Ta kasance matar shugaban majalisar dattawa a jamhuriya ta biyu kuma ta rasu a ranar Talata.
Dakta Saraki, wanda ya kasance gwamnan jihar Kwara har sau biyu, ya tabbatar da rasuwarta a shafinsa na X, inda ya bayyana matuƙar baƙin ciki da miƙa wuya ga ikon Allah.
Ya kuma nuna jin dadinsa da irin kauna, da addu’o’in da ya samu a wannan lokaci na juyayin mahaifiyar tasa.