Featured
Kotu taki amincewa da bukatar korar shugaban EFCC

Babbar kotun tarayya dake Abuja a ranar Laraba, ta kori karar da aka shigar gabanta ana neman ta kori Mista Ola Olukoyede a matsayin shugaban hukumar EFCC.
Da yake yanke hukuncin, mai shari’a Obiora Egwuatu ya kori karar kan cewa mai karar bashi da hurumi ko hakki na shigar da karar.
Kamfanin dillancin labarai na kasa NAN ya rawaito cewa wani lauya mazaunin Abuja, Victor Opatola ne ya shigar da karar yana kalubalantad nadin da shugaban kasa Bola Tinubu yayiwa Olukoyede a matsayin shugaban hukumar EFCC.
Lauyan ya soki nadin shugaban EFCC din ne kan cewa bai cika ka’idar kai adadin shekaru a aiki ba kamar yadda doka ta tanada.