Featured
Sabon Kwamishinan ‘Yan Sanda Salman Dogo Ya Kama Aiki a Kano

Sabon kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano, Salman Dogo Garba ya kama aiki a yau Litinin inda yayi alkawarin samar da tsaro don kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
Salman Dogo ya bukaci hadin kan jami’an rundunar ‘yan sanda da al’umma domin burin da aka sanya gaba.
Yayi bayanin hakan ne a bikin bankwana da wanda ya gada, AIG Mohammed Usaini Gumel.
A nasa jawabin, AIG Gumel ya godewa jami’an ‘yan sanda bisa goyan baya da suka bashi a lokacin aikinsa inda ya bukaci su rubanya hakan ga sabon kwamishinan.
A yayin taron an kuma mika lambar karramawa ga jami’an ‘yan sanda da masu taimakawa rundunar wajen tabbatar da tsaro a jihar.
Haka nan, kungiyar wakilan kafafen yada labarai ta mika lambar karramawa ga AIG Gumel bisa kokarin da ya nuna a lokacin yana kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano.