Featured
‘Yan Najeriya Sama da Dubu 70 ne Suka Sauya Kasa Zuwa Canada

Hukumar kula da shige da fice da ‘yan gudun Hijrah gami da bada shedar zama dan kasa ta kasar Canada IRCC ta ce ‘yan Najeriya 71, 459 ne suka samu shedar zama ‘yan Canada daga shekarar 2005 zuwa 2024.
Hukumar ta IRCC ita ce ke da alhakin kula da lamuran da suka shafi shige da fice zuwa kasar ta Arewacin Amurka.
Najeriya ce ta 10 a jerin kasashen da ‘yan kasar suka sauya kasa zuwa Canada.
Bayanan da ofishin hukumar ya fitar ya nuna cewa yayin da sabbin ‘yan kasar ta Canada suka fito daga kasashe 196 manyan kasashe 10 sun dauke kaso mafi yawa.
IRCC ta ce bayanan ya nuna yawan al’ummar Canada da ake samu.
Bayanai sun nuna cewa kasar India ce kan gaba wajen samar da sabbin ‘yan Canada inda mutane 536, 279 suka sauya kasa daga India zuwa Canada.
Kasar Philippines ke biye da ita da mutane 395, 694.