Featured
Rundunar Sojin Najeriya ta sha alwashin kakkabe ‘yan ta’adda dake kai hare-hare

Shelkwatar tsaron Najeriya ta ce kaddarar ‘yan ta’adda dake haifar da matsalar tsaro a kasarnan za ta kasance gajeruwa a yayin da sojoji baza su gaza ba wajen fatattakarsu.
Darakta janar na shelkwatar tsaron, Manjo Janar Edward Buba, ne ya fadi hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Talata.
Buba ya ce ayyukan rundunar sojan ya kassara karfin shugabancin ‘yan ta’addan da rage musu karfi.
Acewarsa ‘yan ta’addan na kai hari kan fararen hula ne don kare gazawarsu da ta bayyana a fili.
Rundunar sojan ta kuma sha alwashin kakkabe dukkan ‘yan ta’addan dake da hannu a harin garin Gwoza na jihar Borno.
Sannan ta mika ta’aziyya ga iyalan wadanda lamarin ya shafa.