Featured
‘Yan Bindiga Sun Kashe ‘Yansanda 5 A Katsina

‘Yansanda biyar sun rasa ransu yayin artabu da ‘yan fashin daji a karamar hukumar Jibia ta jihar Katsina.
Lamarin ya faru ne a ranar Lahadi da ta gabata yayin da jami’an ‘yansandan ke kan hanyar dawowarsu daga wurin aiki a kauyen Zandam.
Rahotanni sun bayyana cewa an kashe jami’an ‘yansanda 4 nan take a yayin harin. Sai dansanda na 5 da ya rasu a asibitin koyarwa na jihar Katsina.
Haka kuma, ‘yan bindigar sun yi awon gaba da bindigogin AK47 guda 5 na ‘yansandan da suka rasu.
Duk wani yunkuri na jin ta bakin rundunar ‘yan sandan jihar Katsina ya ci tura har zuwa lokacin hada wannan rahotan.