Featured
‘Yan Bindiga Sun Sace Alkaliya Da ‘Ya’yanta A Jihar Kaduna

‘Yan bindiga sun sace wata Alkaliyar karamar kotu dake Sabon Tasha a jihar Kaduna, Janet Galadima tare da ‘ya’yanta 4.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna, Mansir Hassan ne ya tabbatar da hakan inda ya ce an sace Alkaliyar da ‘ya’yanta ne a gidansu dake yankin Mahuta a karamar hukumar Chikun a ranar 24 ga watan Yuni.
Ya ce daga bisani ‘yan bindigar sun kashe babban dan matar mai shekaru 14, Victor Galadima inda ‘yan sanda suka samu gawarsa a Unguwar Bayero dake kauyan Dutse.
Mai magana da yawun ‘yan sandan ya ce sashin yaki da masu garkuwa da mutane na hukumar na aiki da hukumomin tsaro wajen kubutar da alkaliyar da ‘ya’yanta.
Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan bindigar sun kashe dan matar ne bayan gaza biyan kudin fansa.