Featured
KEDCO ya dawo da wutar Jami’ar Aliko Dangote bayan biyan Naira Miliyan 100

Kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na KEDCO ya dawo da bayar da wuta ga jami’ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote bayan biyan Naira Miliyan 100.
Shugaban jami’ar, Farfesa Musa Yakasai ne ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a yau Juma’a.
Ya ce wutar lantarki ta dawo jami’ar da yammancin yau bayan biyan Naira Miliyan 100.
Idan za a iya tunawa dai, kamfanin KEDCO ya yanke wutar makatantar saboda bashin Naira Miliyan 248.
Shugaban jami’ar ya ce an dawo da wutar ne bayan shiga lamarin da gwamnatin Kano tayi da kuma Aliko Dangote wanda ya biya Naira Miliyan 100 ga KEDCO.
Gwamnatin Kano ta bayyana aniyarta na biyan bashin yayin da Dangote yayi alkawarin samar da tsarin amfani da hasken rana wajen samar da wuta a jami’ar.