Featured
Sabuwar Shekarar Musulunci: Gwamnatin Kebbi ta Ayyana Ranar Hutu

Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris ya ayyana Litinin a matsayin ranar hutu domin bikin sabuwar shekara ta addinin Musulunci.
Alhaji Auwal Manu Dogondaji, kwamishinan yada labarai na jihar ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a birnin Kebbi a yau Juma’a.
Acewarsa, ranar Lahadi ne zai zama 1 ga watan Muharram duba da muhimmancin ranar ne gwamnatin ta yanke shawarar dage hutun zuwa ranar Litinin.
Manu-Dogondaji ya taya al’ummar Musulmi murna kan bikin sabuwar shekarar inda ya bukace su da su ci gaba da yin addu’ar zaman lafiya da samun ci gaba a jihar Kebbi da kasa baki daya.