Featured
An sake zaben Tinubu a matsayin shugaban ECOWAS

An sake zaben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a matsayin shugaban kungiyar ECOWAS bayan cikar wa’adinsa na farko.
Wa’adin shugaban kasa Bola Tinubu a matsayin shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika yazo karshe a yau Lahadi.
Ana gudanar da taron kungiyar karo na 65 a Abuja inda ake saran Tinubu zai mika shugabancin kungiyar ga sabon shugaba.
A watan Yuli na 2023 ne aka zabi Tinubu a matsayi a matsayin shugaban kungiyar ta ECOWAS a Guinea Bissau.
Tun bayan lokacin ne dai kungiyar ta fuskanci kalubale da suka hada da juyin mulki a kasashe mambobin kungiyar.