Featured
Yan bindiga sanye da Hijabai sun sace mutane 25 a Katsina

Wasu rukunin ‘yan fashin daji sanye da Hijabai sun kai hari garin Runka a karamar hukumar Safana dake jihar Katsina a daren Asabar inda suka sace mata da kananan yara 25.
Acewar shaidun gani da ido, maharan sun bi gida-gida wajen sace mutanen inda mutum 1 yaji rauni bayan kokarin tserewa.
Shugaban karamar hukumar ta Safana, Sani Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce ana kan kubutar da mutanen.
Duk da cewa rundunar ‘yan sandan jihar Katsina bata magantu kan lamarin ba, baturen ‘yan sanda na karamar hukumar Safana ya tura tawagar jami’ai don taimakawa wajen aikin ceto mutanen.
Lamarin dai ya sake fito da kalubalen tsaro da ake fuskanta a yankin Arewa maso yamma.