Featured
An shiga fargaba yayin da Kura ta tsere daga gidan adana namun daji a Jos

An shiga rudani da fargaba a yankin Dong na karamar hukumar Jos ta Arewa bayan wata Kura ta gudu daga gidan adana damunan daji.
Rahotanni sun bayyana cewa Kurar ta balle daga dakin da ake kulle da ita a ranar Lahadi abinda ya haifar da fargaba ga mazauna Dong da jihohi makota.
Shugaban hukumar yawon bude idanu ta jihar Plateau, Chuwang Pwajok ya tabbatar da hakan ga manema labarai.
Pwajok, wanda ya tabbatarwa da mazauna yankin cewa ana kan kokarin gano Kurar ya ce “Na samu rahotan tserewar Kura daga inda ake ajiye da ita a gidan adana namun daji kuma nan take na umarci ma’aikata da su bibiyeta don gano inda take.”
Shugaban ya kuma musanta zargin cewa Kurar ta tsere ne saboda Yunwa da rashin abinci.