Featured
Dalibai 200 gini ya danne a Jos – Gwamnatin jihar Plateau

A kalla dalibai 200 gini ya danne a makarantarsu da safiyar yau Juma’a a cewar kwamishinan yada labarai na jihar Plateau, Mista Musa Ashoms
Rahotanni sun bayyana cewa ginin makarantar Saints Academy ya rufta ne a kan dalibai yayin da suke zana jarrabawa.
Ashoms, wanda ya ziyarci makarantar tare da sauran kwamishinoni ya ce makarantar tana da adadin dalibai 400.
Kwamishinan ya ce bangaren da ginin ya rufta yana daukar dalibai 200.
“Faduwar ginin ya jawo asarar rayuka kuma ana ci gaba da kwashe daliban da suka jikkata zuwa asibiti. Baza mu iya kayyade adadin daliban da abin ya shafa ba har sai an kammala kwashe su.
” Masu bada agaji suna aikin kokarin ceto. Gwamna Caleb Mutwang ya bada umarnin likitoci su bada kulawa ga wadanda suka jikkata”.