Featured
Kano: Kotu Ta Yanke Wa ’Yan Daba 106 Hukunci A Kwana 10

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da cewa a cikin kwanaki goman, kotu ta kuma ba da umarnin tsare karin wasu ’yan daba 43 a gidajen kangararru na yara.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya kara da cewa laifukan da kotu ta kama ’yan daban da su sun hada da kisa, fashi da makami, raunata jama’a da kuma sace mutane.
Kiyawa ya bayyana cewa wannan ya faru ne a cikin kwanaki 10, daga 24 ga watan Yuni zuwa 4 ga Yuli, 2024.
Kwamishinan ’yan sandan jihar Kano, Salman Dogo Garba, ya yabawa bangaren shari’a bisa rawar da ya taka wajen samun wannan nasara.
Sannan ya yi kira ga al’umma da su rika ba wa ’yan sanda hadin kai da bayanai domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a Jihar Kano.