Featured
Yanzu-Yanzu: ‘Yan Majalisar Wakilai Sun Rage Albashinsu

‘Yan majalisar wakilan Najeriya sun amince su sadaukar da rabin albashinsu tsawon watanni 6 a wani bangare na nuna goyan baya ga ‘yan Najeriya a halin yunwa da kuncin rayuwa da ake ciki.
Hakan ya biyo bayan kudurin da mataimakin shugaban majalisar, Benjamin Okezie Kalu ya gabatar kan bukatar sadaukar da rabin albashinsu na Naira dubu 600 don nuna goyan baya ga ‘yan Najeriya.
Matakin majalisar na zuwa ne a yayin da matasa ke shirin gudanar da zanga-zanga kan halin kuncin rayuwa.