Connect with us

Featured

Gwamnan Kano ya raba taki ga kananan manoma dubu 52, 800

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya kaddamar da rabon taki kyauta na Naira Biliyan 1 ga manoma a jihar a jiya Alhamis.

A sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ya ce rabon takin cika alkawari ne da gwamnan yayi yayin yakin neman zabe kan inganta rayuwar al’umma ta fannin noma.

Acewar sanarwar, a yayin gangamin yakin neman zaben 2023, Gwamna Abba Kabir Yusuf yayi alkawarin bada muhimmanci ga fannin noma.

Sanusi Bature ya bayyana cewa an raba takin na NPK ga kananan manoma 52, 800 a fadin kananan hukumomi 44 na jihar.

Kamfanin samar da taki na jihar Kano wato KASCO ne dai ya samar da takin.

Gwamnan ya ce manoma a yanzu na fama da tsadar kayayyakin noma wanda matsin tattalin arziki ya haifar.

Sannan ya yi bayani kan kudurin gwamnati na ci gaba da samar da takin don saukakawa al’umma.

Wadanda suka amfana da tallafin da suka hada da mata da masu bukata ta mussaman zasu takin na NPK mai girman kilo gram 25 don taimaka musu wajen noma.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet