Featured
Matatar Dangote – Dizal dinmu na da ingancin da za a iya amfani da shi a ko’ina a fadin duniya

Matatar man Dangote ta sake tabbatar da cewa man dizal din da take fitar wa ya cika dukkan wasu ka’idojin da ya kamata dizal ya cika a duniya, musamman idan aka kwatanta shi da wanda ake shigo da shi daga ƙasashen waje.
Wannan dai na zuwa ne bayan kalaman da babban jami’in hukumar kula da harkokin man fetur ta kasa (NMDPRA), Farouk Ahmed ya yi a baya-bayan nan cewa man dizal din matatar Ɗangote bai kai wanda suke shigo da shi ƙasar nan inganci ba.
Jaridar SolaceBase ta ruwaito cewa, babu daya daga cikin dizal din da ake shigowa da shi Najeriya da zai iya yin gogayya da na matatar Dangote ta fuskar inganci.
Haka zalika, duk wanda ke son gwada kayayyakinsu da wadanda ake shigo da su kai tsaye kofa a buɗe take don tabbatar da hakan.
Babban jami’in kasuwanci na rukunonin kamfanin Dangote, Rabiu A. Umar ne, ya bayyana haka ranar Juma’a a Kano a wata tattaunawa da ya yi da manema labarai.
Yace “yace ba ma tsaron a gwada ingancin dizal ɗinmu a ko’ina a duniya, mun fara da 600-700 PPM saboda sabo ne.
“Yanzu dizal din na mu yana kan 87 PPM, kuma a karshen watan Agusta, zai koma 10 PPM.
A cewarsa, ko a lokacin da shugaban majalisar wakilai, Hon. Tajudeen Abbas ya ziyarci matatar man a karshen makon da ya gabata, a kan hanyarsu ta zuwa ne suka yanke shawarar sayen man dizal daga gidajen mai guda biyu, bayan da aka kwatanta da na matatar man Dangote sun yi mamakin sakamakon ingancin dizal din da suka gani.
“Gwajin da aka gudanar a gabansu ya tabbatar da ingancin man dizal din namu kuma ya tabbatar da cewa dizal din namu na daya daga cikin mafi inganci a duniya wanda ke da karancin sinadarin sulfur,” inji Umar.
“Muna samar da dizal mafi kyau a Najeriya. Abin ban takaici ne cewa maimakon a yaba mana, kuma sai ake kushe mana .”