Featured
Ministan ilimi ya umarci shugabannin jami’o’i da su tabbatar da kare dalibai da ma’aikata yayin zanga-zanga

A yayin da matasa ke shirin shiga zanga-zanga a fadin kasarnan, ministan ilimi, Farfesa Tahir Mamman ya umarci shugabannin jami’o’i da su tabbatar da tsaron lafiyar dalibai da ma’aikata a makarantunsu.
Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa wacce mai rikon mukamin shugaban hukumar kula da jami’o’i ta kasa, Chris Maiyaki ya fitar wacce aka rabawa manema labarai a yau Litinin.
Ministan ya kuma bukaci dalibai da su kasance a makarantunsu tare da mayar da hankali ga karatunsu domin kaucewa fadawa hatsari a yayin zanga zangar.
“Gwamnatin tarayya tana sane da hakkin da kowanne dan Najeriya ke da shi wajen gudanar da zanga zangar lumana, amma mun damu da lafiyar ma’aikata da dalibai da makarantu a yayin zanga-zanga.
” A don haka minista ya umarci dukkan shugabannin makarantu da su dau matakai don tabbatar da tsaron dalibai da ma’aikatan jami’a”.