Featured
An kama lakcarorin bogi a jami’ar Bayero dake Kano

Jami’an tsaro na jami’ar Bayero dake Kano sun kama wasu mutane guda biyu da suke kiran kansu a matsayin Malaman jami’ar.
An kama mutanen biyu suna siyar da litattafan karatu na bogi ga sabbin daliban ajin farko.
Acewar sanarwar da sakataren yada labarai na jami’ar, Bala Abdullahi ya fitar ya ce wadanda ake zargin sune: David Iluebe daga jihar Edo da Chike E. Eke daga jihar Delta.
Sanarwar ta bayyana cewa mutanen guda biyu sun shiga dakin bada karatu a tsangayar kere-kere inda suka gabatar da kansu ga daliban ajin farko na sashin kan cewa su Malamai ne.
Sanarwar ta ce mutanen sun bayyanawa daliban cewa siyan litattafan ya zama dole ga duk wanda yake son tsallake darasin.
Sai dai jami’an tsaron jami’ar sun samu nasarar kama mutanen wadanda suka amsa laifinsu.