Connect with us

Featured

Saurayi ya yiwa Budurwarsa wanka da man suyar Awara

Saurayin wata budurwa mai sana’ar awara ya yi mata wanka da tafasasshen mai da take suya da shi a yankin Samarun Zariya da ke Jihar Kaduna.

Matashin ya yi wa buduwar tasa mai suna Hussaina wannan danyen aiki ne saboda ta nemi taka masa burki a wurin sana’arta, lokacin da yake tsaka da daukar awarar da take soyawa yana ci.

Bayan saurayin ya yi ta daukar awara yana dangwalawa a yaji yana ci ne Hussaina ta yi masa magana cewa ya daina, lamarin da ya kai ga cacar baki a tsakanin masoyan.

Amma jama’a da ke wurin suka shiga tsakani aka raba su, shi kuma gogan ya yi tafiyarsa.

Ashe labewa ya yi ba wuce ba, daga bisani kafin su ankara ya zo ya dauki kaskon suyan awarar ya antaya mata tafasasshen man a jikinta.

A halin yanzu dai, iyayen Hisssana, wadanda masu karamin karfi ne da suka dogara da sana’ar, suna rokon jama’a da kungiyoyin kare hakkin dan Adam su kawo musu dauki domin yi mata magani da kuma kwato mata hakki.

Shaidu sun bayyana cewa saurayin da ake zargi ya yi wa budurwar wannan aika-aika ya yi kaurin suna wajen tayar da zaune tsaye.

Wani shaida ya bayyana cewa a kwanakin baya wanda ake zargi ya caka wa wani matsahi almakashi, lamarin da ya yi sanadin mutuwar barin jikinsa.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonCratosroyalbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahisgrandpashabetcasibom xcasibom xgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasibomholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet