Featured
Hukumar DSS ta musanta kai samame ofishin NLC a Abuja

Hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ta musanta kai samame ofishin kungiyar kwadago ta Nijeriya (NLC) da ke Abuja a daren ranar Laraba.
Da Safiyar Alhamis din nan ne Shugaban sashen yada labarai da hulda da jama’a na NLC, Benson Upah, yace jami’an sun kutsa ofishin acdaren jiya Laraba da misalin karpe 8:30, Inda suka tapi da wasu mihamman Takardu.
Sai dai mai magana da yawun hukumar DSS, Dokta Peter Afunanya, yayin da yake mayar da martani, ya ce jami’an hukumar ba su kai wani samame a ofishin NLC ba.
A cewar sa, “Hukumar DSS ba ta kai samame ofishin NLC da ke Abuja ba.”