Featured
Jami’an tsaro sun yi wa ofishin ƙungiyar ƙwadago dirar mikiya

Kungiyar kwadago ta Najeriya NLC ta ce gungun jami’an tsaro dauke da tarin makamai sun yi wa hedikwatarta da ke Abuja dirar-mikiya.
Kungiyar ta ce jami’an sun isa ginin hedikwatar ne da ake kira Labour House, tun da daddare da misalin karfe 8:30
A sanarwar da shugaban sashen hulda da jama’a na kungiyar Benson Upah ya fitar ya ce jami’an sun karya kofar dakin da ke ma’ajiyar littattafai da ke hawa na biyu na ginin inda suke debe daruruwan littattafai da wasu takardu.
Sanarwar ta ce, jami’an sun yi ikirarin cewa suna neman wasu takardu ne da aka yi amfani da su a zanga-zangar matsin rayuwa.
Kungiyar wadda ta ce zuwa yanzu ba ta iya tantance abubuwan da jami’an tsaron suka kwashe ba, ta nemi da a gaggauta janye jami’an daga hedikwatar tata.