Featured
NNPCL Ya Ƙara Kuɗin Fetur A Najeriya

A wata sanarwa da kamfanin ya aike wa manema labarai game da ƙarin kudin, kamfanin ya ce daga yau Talata 3 ga watan Satumban 2024, kamfanin ya ƙara kuɗin litar man fetir daga naira 617 zuwa 897.
Tuni dai wasu gidajen mai a Najeriya suka sauya farashin litar zuwa sabon farashin da kamfanin ya sanar a yau Talata.
Wannan dai na zuwa ne kwana ɗaya bayan da kamfanin na NNPCL ya bayyana cewa yana fuskantar matsalar ƙarancin kuɗi, wani abu da ya sa ƴan Najeriya hasashen kamfanin na koƙarin sanar da sabon farashi ne.
Tun dai bayan da gwamnatin shugaba Tinubu ta sanar da janye tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayun 2023, ƴan Najeriya ke fuskantar sauye-sauye a farashin man wanda kuma ke taɓa sauran sassan rayuwa.