Featured
Tsohon Shugaban PDP A Jihar Sokoto Ibrahim Milgoma Ya Rasu

A cikin wata sanarwa da jam’iyyar ta rabawa manema labarai a yau Laraba 04 ga Satumba, 2024. Ta tabbatar da rasuwar Ibrahim Milgoma bayan ya sha fama da jinya.
Jam’iyyar ta bayyana rasuwar sa a matsayin babban rashi ba ga jam’iyyar PDP ba, rashi ne ga ƙasa baki daya.
Acewar sanarwar “Marigayi Ibrahim Milgoma mutum ne nagari kuma shugaba abin koyi, wanda ya bada gudummawa wajen cigaba Sokoto da ma Najeriya baki daya”.
A karshe jam’iyyar tayi addu’ar Allah ya gafarta masa, ya bawa iyalai da ‘yan uwan sa hakurin rashin sa.