Featured
Gini ya rushe kan wasu mutane a Kano

Wani bene mai hawa biyu yayi sanadin mutuwar wasu mutane guda biyu, yayin da wasu biyu suka jikkata a Jihar Kano.
Benen ya rushe ne da misalin karfe 2 na daren jiya Laraba a unguwar Nomansland dake karamar hukumar Fagge, sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka yi.
Ambaliya ce ta biyo ta bayan ginin bayan daukewar ruwan, wanda yayi sanadiyar rushewar benen, kamar yadda kakakin Hukumar kashe gobara ta jihar Kano Samun Abdullahi, ya bayyanawa manema labarai a yau Alhamis 05, ga Satumba, 2024.
Samun, ya ce an garzaya da waɗanda aka ceto daga benen d ya rushe zuwa asibiti, inda a halin yanzu suke samun kulawa.