Featured
NNPCL zai sayar da Fetur din Dangote kan 1,019 duk lita a jihar Borno

Kamfanin mai na Najeriya, NNPC Ltd ya fitar da jadawalin farashin man da ya sayo daga matatar man Ɗangote.
Bisa ga bayanan da kamfanin ya fitar, farashin zai bambanta daga wuri zuwa wuri a gidajen mai na NNPC a faɗin Najeriya. Inda kamfanin ya bayyana cewa farashin fetur din a Lagos zai kasance N950 kowace lita, yayin da a Sokoto N992, Oyo N960, Kano da Kaduna N999, FCT N992, Rivers N980, sai Jihar Borno wanda farashin zai kai N1,019 kowace lita, wanda shi ne mafi tsada.
NNPCL ta bayyana cewa bisa ga dokar PIA, gwamnati ba za ta ƙara daidaita farashin man fetur ba, sai dai an bar shi ne ga kasuwa ta yi alƙalanci. Haka kuma kamfanin ya tabbatar da cewa an biyan kuɗin man fetur da za a ɗiba daga Matatar Dangote a watan Satumba da kuɗin Amurka dala ($), amma daga ranar 1 ga Oktoba, 2024, za a fara amfani da Naira a duk ma’amalolin ciki.