Connect with us

Featured

Maiduguri: Ɗantata ya ba da tallafin Biliyan 1.5 ga wadanda ambaliya ta shafa

Fitaccen Attajirin nan dan asalin Jihar Kano, Alhaji Aminu Alhassan Dantata, ya bada tallafin Naira biliyan daya da rabi, ga wadanda Iftila’in ambaliya ya shafa a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Dantata ya bada gudummawar ne a yau Talata 17 ga Satumba, lokacin da ya jagoranci wata tawaga daga Kano zuwa gidan gwamnatin Maiduguri domin Ziyarar jajantawa.

Attajirin ya jajanta wa gwamnan Jihar Babagana Umara Zulum, da Gwamnatin jihar, da kuma al’ummar garin Maiduguri musamman wadanda suka rasa yan uwan su yayin ambaliyar.

Dantata mai shekaru 96, yayi addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali ga Jihar Borno da ma Najeriya gaba daya.

A nasa jawabin Gwamnan Jihar Borno, Babagana Umara Zulum, ya mika godiyar sa ga Attajirin saboda nuna damuwar sa ga halin da alummar garin suka shiga a irin wannan lokaci.

“Mutanen Borno suna godiya da irin wannan mutuntawa da wannan dattijo yayi mana, ina tabbatar muku da cewa, Baba ya bamu tallafin N1.5 billion, a matsayin gudummawarsa ga wadanda wannan iftila’i ya shafa, Allah ya maka Albarka ya baka gidan Aljannah, “mun gode Baba”, a cewar zulum.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet