Connect with us

Featured

Ahmad Musa da Shehu Abdullahi za su bugawa Pillars wasa a kakar bana

Yan wasan Najeriya Ahmed Musa, da Shehu Abdullahi, sun dawo kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars a karo na biyu, don taka Leda a gasar Firemiya ta Najeriya na kakar wasa ta 2024/2025.

An hangi yan wasan biyu a cikin tawagar Pillars ne a jiya Alhamip, 03 ga Oktoba a yayin da Kungiyar take atisaye gabanin buga wasa na mako na biyar a gasar Firemiya.

“Ahmed Musa, Shehu Abdullahi, Nazir Laja, da sauran yan wasan kungiyar sun yi atisaye gabannin buga wasan mako na biyar da kungiyar Kano Pillars zata yi a karshen makonnan da kungiyar kwallon kafa ta Sunshine Stars” Kamar yadda kungiyar ta sanar a yau Juma’a 04 ga Oktoba a shafin ta na X.

Musa, mai shekaru 31 ya koma Pillars ne a karo na uku bayan ya taba zama a kungiyar a shekarar 2009/2010 da kuma 2021, Kazalika Abdullahi shi ma ya bugawa kungiyar wasa a shekarar 2012.

Duk da hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta rufe cinikayyar yan wasa ta wannan shekara, amma yan wasan suna da damar buga wasanni, kamar yadda shugaban hukumar Sunday Obaseki ya bayyana, lokacin da aka tambayeshi game da sabbin yan wasan.

“Zamu yi masa rijista, Ahmed Musa zai shiga tsarin cinikayyar yan wasa, babu wata matsala”, a cewa Obaseki.

Share this:
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişGrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetBetwoonRadissonbetcasino siteleriultrabettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasibomjojobetjojobetjojobetjojobet xholiganbet xholiganbetholiganbetholiganbet güncel girişholiganbet xholiganbetgrandpashabetgrandpashabet güncel girişholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabet güncel girişholiganbet güncel girişholiganbet güncel girişgrandpashabet girişsekabetmatbetimajbetcasibompusulabetvdcasinosuperbetincratosroyalbetcasibomholiganbetholiganbet girişholiganbetmarsbahiscasinolevantholiganbetgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet