Featured
Gwamnatin Tarayya Za Ta Gyara Madatsar Ruwa Ta Alau
Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin ta na gyara madatsar ruwa ta Alau, sakamakon lalacewar wani ɓangare na ta, wanda ya jawo ambaliyar ruwa ta baya bayn nan a garin Maiduguri da ke babban birnin Jihar Borno.
Ministan Ruwa da Muhalli, Joseph Utsev ne ya tabbatar da hakan lokacin da ya jagoranci yan kawamitin ma’aikatar sa domin duba halin da madatsar ruwan take ciki.
Read also:Borno: Wani Sufetan Dan Sanda A Maiduguri Ya Hallka Kansa
Ministan wanda Darakta mai kula da bangaren madatsun ruwa, Malam Aliyu Dala, ya wakilta yace, za a fi mayar da hankali wajen gyara bangaren da ya haifar da Iftila’in, da kuma kewayen madatsar gaba daya.
A karshe yace tuni Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bada umarnin kafa kwamitin da zai binciki halin da madatsun ruwa suke a fadin kasar nan.
