Featured
Gwamnatin Kano Ta Sallami Ƴan Jaridar Gidan Gwamnati

Gwamnatin Jihar Kano ta sallami yan jarida 14, wadanda suke daukar rahoton aiyukan gwamnatin, inda ta bukaci su koma kafafen yada labarun su.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sanusi Bature Dawakin-Tofa, ya aikawa yan jaridar da abin ya shafa a jiya Litinin 21, Oktoba 2024, ta cikin Whatsapp group na yan jaridar gidan gwamnatin jihar, ya bukaci su koma kafafen yada labarun su domin maye gurbin su, duk da ba’a bayyana wani dalilin game da korar ta su ba.
A cewar sa, “ina matukar godiya gareku bisa aikin da muka yi da ku tsahon shekara ɗaya da ƴan watanni, a lokacin da na yi tafiya Jamhuriyar Serbia a makon da ya gabata, wasu batutuwa sun faru, kuma shugabanni sun yanke shawarar daukar wasu matakai”.
Sanarwar ta fitar da sunayen ‘yan jarida 14 da abin ya shafa, wadanda suka hadar da: Aliyu Yusuf, Daraktan Wayar da Kan Jama’a ’a. Sani Suraj Abubakar, PRO, Adamu Dabo, Chairman Press Crew, FRCN- Naziru Yau, ARTV, Sadiq Sani AA, ARTV, Rabiu Sunusi, Triumph, Umar Sheka, Freedom, Jabir Dan ‘abba, Nasara, Labaran Sound- Simon, AIT, Cameraman- Nasiru Danhaki, NTA, Abdullahi Sule, Driver, Murtala Baba Kusa, Express, da kuma Ibrahim Muazzam, Radio Kano.