Featured
Rundunar ƴansndan jihar Kano tace za ta yi biyayya ga umarnin kotu a zaɓen ƙananan hukumomi

Rundunar Yan Sandan Jihar Kano ta ce zata yi biyayya ga umarnin kotu, wanda ya dakatar da ita sanya hannu a zaben kananan hukumomin jihar da za a gudanar a ranar Asabar 26 ga Oktoba 2024.
Mai magana da yawun Rundunar Yan Sandan jihar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana hakan ta cikin wani faifan bidiyo da ya fitar.
“Akwai umarnin kotu da aka bawa rundunar yan sanda, kuma a cikin lamaba ta 9 na wannan umarni ya bayyana cewa yan sanda kada su bayar da tsaro a wannan zabe, don haka za mu yi biyayya ga umarnin kotu”.
“Dan haka Rundunar Yan Sanda ba za ta sanya hannu a wannan zabe da za a gudanar ba, amma hakkin mu ne mu tabbatar da tsaro da doka a Jihar Kano, kuma ba za mu lamunci duk wani mai son karya doka ba”, a cewar Kiyawa.