Connect with us

Featured

Gwamnan Kano Ya Cika Alƙawarin Biyan Sama Da Miliyan 11 Ga Iyalan Marigayi Salisu Yaro

Gwamnan jihar Kano Abba Kabiru Yusuf, ya cika alkawarin biyan sama da naira Miliyan 11 ga iyalan Marigayi Alhaji Salisu Yaro, tsohon jami’in walwala na kungiyar Kwallon kafa ta Kano Pillars.

Gwamnan ya bayar da chakin kudin ne ga iyalan Marigayi Yaro, ta hannun kwamishinan matasa da wasanni Mustapha Rabiu Kwankwaso.

Mustapha Kwankwaso, wanda ya ziyarci gidan Marigayi Salisu Yaro a ranar Juma’a, ya mika chakin kudin ga iyalan Marigayin domin suyi amfani dasu wajen kula da rayuwarsu.

A baya dai Alhaji Salisu Yaro, ya kasance babban jami’i a kungiyar Kwallon ƙafa ta Kano Pillars, wadda ya hidimtawa tsawon shekaru kafin rasuwarsa a farkon shekarar da muke ciki.

To sai dai Gwamnatin Kano ƙarƙashin jagorancin gwamna Abba Kabiru Yusuf, ya ga dacewar biyan hakkokin da Marigayi Yaro yake bi a kungiyar ta Kano Pillars.

Lamarin da ya sanya a ranar Juma’a, kwamishinan matasa da wasanni na Kano Mustapha Rabiu Kwankwaso ya ziyarci gidan Marigayin tare da mika chakin kudin ga iyalan nasa.

Haka zalika Mustapha Kwankwaso ya kara da cewa, a baya ma sun biya wasu da dama hakkokinsu cikin waɗanda suka hidimtawa kungiyar ta Kano Pillars.

Ya kuma ce, da sannu sauran waɗanda suka hidimtawa kungiyar ta Kano Pillars, Gwamna Abba Kabiru Yusuf zai biya su hakkokin da suke bi.

Share this:
Exit mobile version
meram escorttrlisans pinterestgiftcardmall/mygiftgrandpashabet girişgrandpashabet güncel girişgrandpashabetgrandpashabet girişgrandpashabettaraftarium24dizipalgiftcardmall/mygiftjustin tvGrandpashabetGrandpashabetGrandpashabetcasino siteleriRadissonbetsweet bonanzacasino siteleripadişahbettaraftarium24taraftarium24rojadirectajustin tvcasinolevantjojobetjojobetjojobetcasibomholiganbet xcasinolevantcasinolevantjojobetjojobetholiganbetholiganbetholiganbetholiganbetjojobetgrandpashabetmatadorbetonwinsahabetgrandpashabetmarsbahis xmarsbahiscasinolevantcasinolevantcasinolevantgrandpashabetjojobetjojobetgrandpashabetsekabetmatbetimajbetmatbetimajbetpusulabetvdcasinosahabetmarsbahismarsbahis girişholiganbetholiganbet girişcasibomcasinolevantjojobetcasinolevantgrandpashabetgrandpashabetnesinecasino xwbahis xbetgaranti xtambet xgrandpashabet girişGrandpashabetjojobet